Shugabanin kasashen Afrika na ci gaba da tattaunawa da hukumomin kasar Rasha a wuni na biyu na taron da suke gudanarwa a birnin Sochi da nufin karfafa hulda a fannoni da dama wadanda suka hada da sha’anin ma’adanai kasuwanci noma da kiwo da kuma matsalar tsaron da ta addabi galibin kasashen nahiyar ta Afrika.
Ministan watsa labaran Jamhuriyar Nijar Salissou Mahaman Habi, ya ce wannan wata dama ce da Afrikar ta samu don gwadawa duniya cewa kan mage ya waye.
Lura da yadda manyan kasashen yammacin duniya da wasu takwarorinsu na nahiyar Asiya suka yi wa nahiyar Afrika ca da sunan sabon salon huldar diflomasiyya, ya sa kasar Rasha sake jan damara da nufin kyautata dadaddi
Batun tsaro na daga cikin mahimman batutuwan da kasashen na Afrika ke da damuwa akansu musamman ta’addancin da ya addabi yankin Sahel saboda haka ake ganin taron na iya zama wata damar tattaunawa hanyoyin odar makaman yaki a wajen wasu kasashen.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma domin jin karin bayani: