Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus dan kasar Putugal ya sanya katafaren gidan da ya mallaka da ke birnin Manchester a kasuwa.
Hakan bai yi wa magoya bayan Manchester United dadi ba, musaman wadanda ke sa ran Cristiano Ronaldo zai iya dawowa kungiyar wani lokaci nan gaba.
Kafin komawar Ronaldo Juventus daga Real Madrid, a farkon kakan wasan bana, wasu kafofin yada labarai sun sha ruwaito cewa, akwai yiwuwar tsohon dan kwallon Manchester United, kuma tsohon gwarzon dan wasan Duniya ya koma kulob din na Manchester United, da taka leda bisa hasashen anan zai ajiye takalmansa.
A shekara ta 2006 ne Ronaldo, ya sayi gidan a yankin Cheshire na kasar Ingila, lokacin da ya ke haskakawa a kungiyar ta Manchester United, karkashin jagorancin kocinta Sir Alex Ferguson, wanda ya sayoshi daga Sporting Lisbon, na kasar Putugal.
Ronaldo dai ya sayi gidan ne akan kudi fam miliyan £3 da dubu 85, kuma wannan ba shi ne karo na farko da dan wasan yake yunkuri wajen saida gidan nasa ba, domin a shekarar 2009, lokacin da ya koma kungiyar Real Madrid, na kasar Spain ya sanya shi a kasuwa amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Ka tafaren gidan ya kunshi dakunan kwana guda biyar, da wajan motsa jiki (Gymnasium) da kuma wajan ninkaya ( Swimming pool) da dai sauran nau'in wasu abubuwan more rayuwa.
Facebook Forum