Shugaban kamfanin Google ya yi kira akan bukatar samar da matakan daidaita bayanan sirri.
Wannan kiran na zuwa ne a lokacin da yake ganawa da hukumomin kasashen Turai cewa fasahar tana kawo fa'ida a bangare daya, kuma tana haifar da "mummunan sakamako."
Kalaman na Sundar Pichai na zuwa ne yayin da 'yan majalisar dokoki da gwamnatoci suka yi la’akkari da sanya iyaka kan yadda ake amfani da bayanan leken asirin.
"Babu tababa a cikin raina cewa akwai bukatar a tsara bayanan leken asirin. Tambayar ita ce; ta ya ya za a iya fuskantar wannan," in ji Pichai, a wata sanarwa da ya yi a cibiyar tunawa da masana’antar ta Brussel.
Ya ce akwai muhimmiyar rawar da gwamnatoci za su taka, kuma yayin da Tarayyar Turai da Amurka suka fara tsara nasu hanyoyin aiwatar da ka'idoji, ''daidaitar na kasa-da-kasa na duk dokokin da za su faru nan gaba za su yi matukar muhimmanci.
Amma bai shaida wata hanya daya tilo da za’a bi ba.
Pichai ya yi magana ne a ranar da aka shirya zai hadu da jiga-jigai kuma masu fada a ji a kungiyar kasashen Turai.
A shekarun baya, Vestager ta ci tarar Silicon Valley da zunzurutun kudade biliyoyin dalar Amurka, saboda zargin da ake masu na cin zarafin kasuwar fasahar zamani.
Bayan an sake zabarsa zuwa wa’adi na biyu na kaka mai zuwa tare da fadada iko akan manufofin fasahar dijital, yanzu Vestager ta zura idanun ta a kan sirrin wucin gadi, kuma tana tsara ka'idoji kan amfani da ita.
Facebook Forum