Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Sake Bitar Farashin Kujerun Aikin Hajji a Najeriya


Masu aikin hajji a Saudiyya.
Masu aikin hajji a Saudiyya.

Yayin da ‘yan Najeriya musamman maniyyata aikin hajjin bana ke ci korafi da game farashin kujerar aikin hajji da hukumar alhazan kasar ta kayyade, na fiye da naira miliyan guda da rabi ga kowane Alhaji.

Masana harkokin aikin Hajji da Umara a kasar na bayyana bukatar dake ga gwamnati ta sake bitar farashin kujerun aikin hajjin da nufin saukakawa maniyyatan na bana.

A hira da wakilin Muryar Amurka yayi da Ambassador Usman Darma, mataimakin shugaban cibiyar kasuwanci da masana’antu ta jihar Kano kuma shugaban kamfanin shirya zirga zirga na Darma Air ya danganta lamarin da sakaci daga banagaren gwamnatin tarayya.

Ambasada Usman ya ce sunyi nazari kan yadda kudaden zuwa aikin hajji zasu kasance, inda yace tun daga kan kudin jirgi zuwa masauki da guzuri baki ‘daya kudin da yakamat Alhazai su biya shine Naira Miliyan ‘daya da dubu dari biyu, maimakon Naira miliyan daya da rabi.

A cewar Ambasada rashin saka ido ne ya haifar da wannan matsala ta hauhawar farashin kujerar aikin hajjin bana, inda yace ya kamata gwamnati ta rika tabbatar da cewa hukumar da ke da alhakin wannan aiki tana yin aikin da yakamata.

Domin karin bayani ga tattaunawar wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari da Ambasada Usman Darma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG