‘Yan gwagwarmaya sun ce jami’an tsaron Syria ko Sham sun hallaka mutane akalla 32 a jiya Jumma’a, a sa’ilinda masu sa ido na kungiyar kasashen Larabawa ke ziyartar wurare don ganin ko gwamnatin kasar na aiwatar da alkawarinta na kawo karshen gallaza wa ‘yan tawaye.
Kwamitin tafi da harkokin ‘yan adawan na Sham ya ce akasarin mace-macen sun auku ne bayan da jami’an tsaro su ka bude wuta kan masu zanga-zangar adawa da gwamnati a wurare da dama.
‘Yan gwagwarmayan da kuma shaidu sun ce dubun dubatan mutane sun yi gangami a fadin Sham inda su ka sake kiraye-kirayen Shugaba Bashar al-Assad ya sauka.
A halin da ake ciki kuma kamfanin dillancin labarai mallakin gwamnati mai suna SANA a takaice, ya nuna hotunan magoya bayan Mr Assad na kada tutoci a gangamin hadin kan kasa da aka yi a birane, ciki har da Damascus da Homs.
Kamfanin dillancin labaran ya kuma ce wani ayarin masu sa ido na kungiyar kasashen Larabawa sun ziyarci wasu unguwanni a Hama, inda a wasu lokutan ma su ka rinka ziyartar asibitoci don ganawa da wadanda su ka sami raunuka.
Kamfanin dillancin Labaran ya ce wasu tawagogin kuma sun ziyarci unguwannin bayan garin birnin Damascus da kuma wasu wurare a yankin Homs. Kimanin masu sa ido 60 ne ke kasar.