Dan wasan tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya kuma jagora a kungiyar Super Eagles Ahmed Musa, mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Al'Nassr dake kasar Saudi Arebiya ya lashe kofin Super Cup na Saudi.
Musa ya samu nasarar ne a ranar Lahadin din da ta gabata, bayan da suka samu nasara akan kulob din Al'Taawon da ci 5 da 4, a bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalty), bayan da aka tashi canjaros 1-1 a filin wasan Sarki Abdullah (King Abdullah).
Wannan ne karo na biyu da Musa yake lashe kofin tare da tawagar kwararru na kungiyar Al-Nassr na kasar Saudiya.
A lokacin wasan, dan wasa Abdulfattah Mohamed Adam, shi ya canji Ahmed Musa ana saura mintuna biyar a tashi daga wasan.
Dan wasan gaba na AT Taawon, mai suna Leandre Tawamba dan kasar Kamaru, shi ya fara jefa kwallo a ragar Al-Nassr, a cikin mintuna 18 da fara wasan, daga bisani Abderrazak Hamdallah ya rama mata ana saura minti biyu a tafi hutun rabin lokaci.
Facebook Forum