Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afghanistan:Taliban Zasu Dinga Kai Hare-Hare Har Sai Dakarun Amurka Sun Fice Daga Kasar


Gawarwakin sojojin Afghanistan da 'yan Taliban suka hallaka wannan watan
Gawarwakin sojojin Afghanistan da 'yan Taliban suka hallaka wannan watan

Cikin 'yan kwanakin nan 'yan kungiyar ta'addanci ta Taliban tana kara kai hare hare a sassa daban daban cikin kasar Afghanistan

Kungiya Taliban ta kaddamar da zazzafan harin da tayi wa lakabi da “Kakar Hari” a Kasar Afghanistan , inda tace zata kai hare haren ne kawai akan Dakarun Amurka dake Jagorancin Mamayar kasar har sai sun janye”

A wani bayani da suka bayar a yau Jumma’a ga manema labarai, Yan kungiyar sun ce wannan farmakin da suka yi wa lakabi “Operation Mansouri” zai fara aiki a yau Jumma’a a dukkanin yankuna 34 dake cikin Afghanistan.

Mai Magana da yawun ministan tsaro Mohammad Radmanesh ya yi watsi da sanarwar hare haren inda ya kira ta da sunan wata sabuwar farfaganda ta yan tsagerun da suke son fada kan fararen hula. Ya fadawa Muryar Amurka cewa dakarun Afghanistan a shirye suke kamar yadda suka yi a shekarun bayan wajen tarwatsa Yan kungiyar ta Taliban da kuma wannan sabon shirin nasu da suka kira “Operation Mansouri

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG