Rahoton da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa ta NCDC ta fitar a baya-bayan nan ya nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya a yanzu ya kai 232.
Jihar Legas ce a kan gaba a cikin jihohi akalla 13 da cutar ta bulla. A halin da ake ciki kuma, mutane 33 sun warke daga cutar har an sallame su daga asibiti, bayan haka wasu su 5 sun riga mu gidan gaskiya.
Daga cikin wadanda suka warke daga cutar, sun hada da wani yaro dan shekara 10 da haihuwa, wanda shine mafi karancin shekaru ya zuwa yanzu.
A yayin da kwararru ke kokarin laluben maganin wannan cuta ta COVID-19, likitoci na ci gaba da bada shawarwari akan matakan kariya daga cutar, musamman wanke hannu akai-akai. Sadiq Aliyu Hussaini, kwararren likita ne a Najeriya, ya jaddada muhimmancin yin nesa-da-nesa da juna.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum