Wakilin Muryar Amurka ya zaga Birinin Abuja saboda ya gano ma idanunsa irin masifar da karancin man fetur ya jefa jama'a ciki.
Wadanda wakilinmu ya zanta dasu a babban gidan man fetur da ake kira mega sun bayyana halin da suke ciki sabili da karancin man.Wani Lawal yace mai yana mugun karanci a garin inda yace su tun safe suka fito gashi har faduwar rana basu sami man ba. Shi ma Ado Abubakar yace suna shan wahala akan rashin mai a Abuja da kewaye.
Rashin mai ya hana mutane yin aikinsu musamman masu jigilar mutane a cikin birnin. Wasu sun bar ayyukansu na kullum sun shiga neman mai. Wakilinmu yace dogayen layuka ne suka mamaye gidajen mai kalilan dake sayar da man. Wasu mafi yawan gidajen man basa ma sayar dashi gaba daya.
Duk da mugun karancin man kamfanin man Najeriya NNPC yace yana da isasshen man da 'yan Najeriya zasu sha na har tsawon kwanaki ashirin da bakwai bisa ga yin anfani da lita miliyan arba'in duk rana. Kamfanin yace yana daukan matakan kawo karshen matsalar.
Inji kamfanin, yajin aikin da kungiyar masu dakon mai da direbobin dakon man bisa dalilan bashin da suka ce suna bi ya haddasa karancin man. Gwamnati ma tace akwai isasshen mai kuma a shirye take ta biya basukan da ake binta. Ministar kudi tace sun biya dillalan mai nera biliyan 350 a watan Disamba.Sun kuma biya gibin dake akwai na nera biliyan 31. Yanzu tana shirin ta sa hannu a biyasu wasu kudin nera biliyan 156.
Ga rahoton Hassan Kaina Maina