Na farko babu abun da kasar take yi. Komi shigo dashi a keyi.Kifi, sukari madara da sauransu duk ana shigo dasu ne. Babu dalilin yin hakan domin kasar tanada albarkatun kasa da zata samu hanyar yinsu cikin gida. Kasar da ta rayu akan shigo da kaya dole ta samu matsala.
Abu na biyu inda kasar ke samun kudin shiga shi ne man fetur. Yanzu farashin man fetur ya fadi dole kuma kudin shiga ya ragu. Kudin dake shigowa ya ragu amma kuma duk abubuwan da kasar take anfani dasu na kasashen waje ne. Dole ne darajar nera ta fadi.
Sai lokacin da kasar ta dage tana abubuwa da kanta san nan darajar nera zata farfado. Ban da haka dole gwamnati ta daina tallafawa nera. Duk lokacin da aka tallafawa nera to ana taimakawa mutane ne su dinga sayen kayan waje domin zai zo masu da araha. Amma da an daina tallafawa nera ita zata samar ma kanta matsayi. Mutane da kansu zasu dawo suna sayen na gida.
Da zara mutane sun soma sayen kayan gida za'a samu aikin yi, kasuwanci zai habaka, nera kuma zata samu daraja.
Kasuwanci zai taimaka wurin samun kudin shiga. A dauki misalin kamfunan waya. Kamfanonin sun dauki ma'akata dubbai. Wasu ma sun kirkiro tasu sana'ar irin masu sayar da katin waya kawai. Waya tayi taimako. Yanzu babu mai barin gidansa zuwa wani wuri sai ya buga waya domin kada ya yi tafiyar banza. Saboda wayar wani harkar kasuwanci ma ta waya ake yi ba sai an yi tafiya ba. Duk wannan ya taimakawa tattalin arziki..
Gwamnati ta duba wasu hanyoyin. Gwamnati bata da hurumin gina hanyoyi. A bar 'yan kasuwa su nemo jari su ginasu daga baya su samu kudinsu daga harajin da mutane zasu biya. Idan aka ba dan kasuwa dama daga koina zai nemo kudinsa ya saka jari.\
Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.