Idan da sauro na yada HIV kamar yadda yake yada cutar cizon sauro, miliyoyin ‘yan Nigeriya lallai zasu rasa rayukansu kullun, musamman a kasashe masu tasowa kamar Nigeriya inda sauro yayi yawa.
Da an sami ruhotanni game da yiwuwar cewa sauro zai iya yada kanjamau, duk da haka, masana sunce, koda yake sauro yana cizo kamar yadda ake iya dibar jini ko kuma sa magani da allura, duk da haka sauro baya iya yada kanjamau ba.
Wani kwararre mai ba cibiyar yaki da ciwon sauro ta Amurka shawarwari Joe Conlon ya bayyana cewa, ko da yake sauro yana daukar kwayar cutar kanjamau da kuma sauran cututtuka na jini, baya iya yada kanjamau.
Conlon ya tabbatar cewa da farko idan sauro ya cije ka, yana jan jinin mutum zuwa cikin jikinsa inda wani ruwan halitta dake cikin jikinshi yake kwayar HIV domin kwayar HIV tana mutuwa nan da nan. Bisa ga cewarshi, koda maganin dake cikin sauron bai yiwa kwayar kome ba, ba zata iya fitowa daga cikin sauron ba.
Dalilin shine, domin sauro na amfani da wadansu abubuwa kamar bututu guda biyu wajen dibar jinni da kuma ya sawa mutum miyau domin kada jinin da yake ja ya bushe yayinda yake sha to wannan miyau yana kashe kwayar cutar HIV yasa ko da ya sake cizon wani mutum ba zai iya daukar cutar ba.
Conlon ya bayyana cewa, “Kamin sauro ya yada cuta, dole ya dauki kwayar cutar. Kwayar cutar dole ta rayu a cikinsa ta kuma ratsa jikinshi ta fito ta miyaun sauro, Wannan wata hanya ce mai wuya sosai, kuma kanjamau baya iya rayuwa a nan.”
Kwayar sauro, kuma, tana rayuwa a cikin sauro, daga nan sai ta wuce zuwa miyonsa domin ta cigaba da rayuwa a jikin wani mutumin.
Kwayar cutar kanjamau bata yawo da yawa cikin jinni kamar yadda kwayar zazzabin cizon sauro take yaduwa, saboda haka sauro baya daukar kwayar cutar HIV da yawa daga wanda yake dauke da cutar zuwa wani.
Koda ace haka zata iya yiwua, sai kimanin sauro miliyan 10 sun ciji wanda yake dauke da cutar HIV a hada dukan jinin da suka ja kafin kwayar cutar ta isa wani ya iya sawa daukar cutar.