Bayanai na ci gaba da bayyana dangane da abin da ya haddasa faduwar jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban Najeriya Prof. Yemi Osinbajo a ranar Asabar.
Osinbajo ya je yankin Kabba a ne a jihar Kogi domin yakin neman zabe a lokacin da jirgin mai saukar ungula ya yi saukar gaggawa.
Rahotanni sun ce, kamfanin da aka dauki hayan jirgin mai suna Caverton Helicopter, ya ce, yanayin hazo da ya mamaye sararin samaniya ne ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.
Babu dai wanda ya jikkata a wannan hatsari.
Tuni mataimakin shugaban kasar na Najeriya, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, suna ciki koshin lafiya, tare da mika godiya ga wadanda suka nuna alhininsu dangane da wannan lamari.
“Mun yi amannar cewa Allah zai ci gaba da kare mu da Najeriya yayin da muke kokarin ciyar da kasar gaba.” Osinbanjo ya wallafa a shafinsa na Twitter.