Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Amurka Ta Ce Kan Jita-jitar Mutuwar Shekau


Shugaban Amurka Joe Biden, ranar Alhamis 20 ga watan Mayu 20, 2021, a Washington. (AP Photo/Evan Vucci)
Shugaban Amurka Joe Biden, ranar Alhamis 20 ga watan Mayu 20, 2021, a Washington. (AP Photo/Evan Vucci)

“Ko da an kashe Shekau, har yanzu ayyukan ta’addanci za su ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya a yankin,” kakakin ya fadawa VOA, yana mai nuni da cewa, “ba Boko Haram ba ce kadai take gudanar da ayyukanta a yankin.

Amurka ta ce ba za ta bayyana cewa shugaban kungiyar Boko Haram ya mutu ba, duk da rahotanni da ke nuna hakan.

“Amurka ba ta tabbatar da wadannan rahotanni ba tana kuma ci gaba da bibiyan al’amuran da ke faruwa,” kakaki a Fadar Gwamnatin Amurka ta White House a majalisar tsaron kasar ya fadawa VOA a ranar Juma’a.

Jami’in ya fadi hakan ne bayan da aka tambaye shi makomar dadadden shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

A farkon makon nan rahotanni a kafafen sada zumunta suka bayyana cewa Shekau ya mutu inda wasu ke cewa ya gamu da ajalinsa ne a lokacin wata arangama da suka yi da mayakan ISWAP a dajin Sambisa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wasu daga cikin rahotannin sun ce Abubakar Shekau ne ya harbe kansa, ko kuma ya tayar da bam a jikinsa, bayan da aka kama shi aka kuma nemi ya yi mubaya ga kungiyar ta IS.

Karin bayani akan: ISWAP, ​Boko Haram, Amurka, Abubakar Shekau, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Kakakin sojin Najeriya ya fadawa manema labarai a ranar Juma’a cewa, suna kan bincike don tantance sahihancin rahoton, amma wasu jami’ai da masu fashin baki sun ce a yi hattara da rahotanni, lura da cewa an sha cewa an kashe shi amma kuma sai ya sake bayyana daga baya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ya fada a wani lokacin daban cewa, ma’aikatar na aiki don gano asalin gaskiyar lamarin, inda ya ce, idan har lamarin ya tabbata, “mutuwar daya daga cikin babban dan ta’adda a tarihin Afirka zai zama babban ci gaba.”

Sai dai duk da haka, jami’in ya nemi a yi taka-tsantsan, domin a cewar shi, mutuwar Shekau kadai, ba abin a yi murna ba ne.

“Ko da an kashe Shekau, har yanzu ayyukan ta’addanci za su ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya a yankin,” kakakin ya fadawa VOA, yana mai nuni da cewa, “ba Boko Haram ba ce kadai take gudanar da ayyukanta a yankin.

XS
SM
MD
LG