A Yau Jumma'a 21 ga watan Yunin shekarar 2019, za'a fara gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar kasashen Afrika AFCON 2019, wanda kasar Masar zata karbi bakoncin ta.
Mai masaukin baki Masar ce za ta bude gasar tsakani ta da kasar Zimbabwe, wasan za'a bugane da misalin karfe Tara na yammaci agogon Najeriya da Nijar.
A karon farko kenan da kasashen Afrika 24 zasu fafatawa a wannan gasar, inda manazarta ke ganin, cewa akwai yiwuwar mai masaukin baki Masar ta sake lashe gasar a karo na 8 duk da cewa, za ta fuskanci babban kalubale daga takwarorinta.
Masu shirya gasar sun ce, an tanadi dukkan abubuwan da ake bukata na gudanar da gasar cikin armashi, duk da cewar a kurarren lokaci kasar Masar ta samu izinin karbar bakoncin gasar.
A bangare guda, za a bude gasar ce ta cin kofin Afrika kwanaki kalilan da rasuwar tsohon shugaban kasar Masar, Mohamed Morsi, wanda wasu ke ganin cewar za'a iya daga wasan sai dai kasar ta Masar tace ko kadan rasuwar tasa ba zata shafi wasan ba.
Facebook Forum