A kudu maso gabashin kasar Turkiya an kashe akalla jami'an 'yansanda uku a wani mummunan hari biyo bayan rikicin da aka kwashe makonni da dama ana yi tsakanin dakarun gwamnati da mayakan kurdawa.
Majiyoyi biyu sun ce an kashe jami'an 'yansanda biyu cikin wata mota da bom ya tashi kusa da ake binciken ababen hawa a garin Sirnak. Jami'an tsaro sun fatattaki maharan da jirgi mai tashin angulu kuma sun samu nasarar kashe biyu ckinsu yayinda sauran suka arce.
An kashe jami'in 'yansanda na ukun a garin Silvan dake gundumar Diyarbakir bayan 'yan jam'iyyar kurdawa da ake kira Kurdish Workers Party ko PKK a takaice sun kai hari da rokoki.
Cikin makonnin da suka gabata dakarun tsaron Turkiya sun kai hare hare da dama a kudu maso arewacin garin Cizre.
Bayan da aka dage dokar hana fita ta kwana tara mazauna garin sun fito sun ga gidaje da motoci da harsashai suka zanesu kuma koina suka juya fankon albarusai suke gani.