Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Legas Ma'aikata Sun Yi Watsi da Kiran Shiga Yajin Aiki da ULC Ta Yi


Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode
Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode

Yayinda kungiyar ULC ke buga kirjin aiwatar da yajin aikin gama gari na ma'aikatan Najeriya , su kuwa ma'aikatan jihar Legas watsi suka yi da kiran suka cigaba da ayyukansu kamar yadda yajin aikin bai yi tasiri ba a duk fadin kasar.

Ma'aikatan kwadagon Najeriya musamman a jihar Legas sun yi watsi da kiran da United Labor Congress ko ULC ta yi na cewa su fara yajin aikin gama gari na har "sai baba ta gani".

Alamu sun nuna cewa ma'aikata da dama sun fita zuwa wuraren ayyukansu musamman a bankuna da gidajen mai da filayen jiragen sama. Bankuna sun kasance a bude kuma kwastamominsu na shiga da fita. Yawancin ma'aikatan sun ce basu da labarin wani yajin aiki.

Kodayake ministan kwadago Dr. Ngige ya ce kungiyar ta ULC haramtaciya ce saboda bata da rajista amma shugabanta Mr. Ajero ya ce bata bukatar amincewar ministan domin samun halarci a kasar. Ya cigaba da cewa ko kungiyar TUC sai da ta gudanar da ayyukanta na tsawon shekaru 27 kafin ta samu rajista amma hakan bai hanata gudanar da ayyukanta ba.

'Yan Najeriya na ganin cewa kiran yajin aikin na son kai ne kawai saboda haka ba zai yi wani tasiri ba.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG