Wata kungiyar ‘yan mata a Afrika ta Kudu su 20 da ake kira U-Dream Global Team sun kera wani jirgin sama mai daukar mutane 4, da yanzu haka yake zazzaga nahiyar Afrika. Kwararru a fannin jiragen sama na ganin wannan a matsayin wani gagarumin ci gaba, wanda zai karfafa gwiwar matasa dake sha’awar zama matukan jirgin sama, ko aikin injiniya.
Daya daga cikin ‘yan matan, Megan Werner ‘yar shekaru 17 da haihuwa, bata da ko lasin tuka mota, amma sai gashi tana daya daga cikin wadanda suka kera jirgin sama. A satin da ya gabata ne ‘yan matan suka bar babban birnin kasar Afrika ta Kudu zuwa kasar Masar.
Agnes Semeela, daya daga cikin ‘yan matan wadda ta taka rawar gani wajen hada wannan jirgin ta ce tana da kwarin gwiwar cewa jirgin zai je kasar Masar, ya kuma koma Afrika ta kudu lafiya. Ta kuma ce tabbas kungiyarsu ta yi kokari sosai wajen kera jirgin da sarrafa shi.
Kungiyar matasan ta U-Dream Global Team za ta yi zagayen kasashen Afrika, wato tafiya mai tsawon kimanin kilomita 12,000 kuma zasu sauka a kasashe 11.
Facebook Forum