Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Texas Kudancin Amurka An Cafke Masu Tallata Karuwanci da Safarar 'Yan Mata


 Carl Ferrer shugaban kamfanin dake tallata karuwaanci da safarar 'yan mata
Carl Ferrer shugaban kamfanin dake tallata karuwaanci da safarar 'yan mata

‘Yan sanda a Jihar Texas da ke Kudancin Amurka, sun cafke shugaban wani shafin da ake zargi da tallata ayyukan karuwanci da safarar ‘yan mata, mai suna Backpage.com.

An cafke Carl Ferer ne da wata takaradar iznin kama shi da hukumomin California suka bayar, bayan da ya isa birnin Houston da ke jihar ta Texas, yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Amsterdam.

Babbar Attorney Janar din California, Kamala Harris, ta na zargin Ferrer da wasu abokanan huldarsa, da kafa shafin mata masu zaman kansu, wanda ya shahara a duniya, tare da baiwa masu aikata manyan laifukan damar tallata ayyukan ashsha a shafin.

A zahiri an yiwa shafin na Backpage.com rijista a matsayin shafin tallata ‘yan rakiya ga baki, amma kuma akan tallata kayayyaki da ayyuka a kansa.

Hukumar da ke karban haraji ta ce shafin na Backpage.com ya samu kusan Dala miliyan 51 a jihar ta California kadai a tsakanin watan Janairun shekarar 2013 zuwa watan Maris din shekarar 2015.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG