Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Taraba Wani Jami’in DSS Ya Harbi Wani Magidanci


Inda jami'in DSS ya harbi mutumin a Jalingo, jihar Taraba
Inda jami'in DSS ya harbi mutumin a Jalingo, jihar Taraba

Yanzu haka al’umma da kungiyoyin kare hakkin dan Adam a jihar Taraba sun bukaci hedikwatar rundunan tsaron farin kaya ta DSS da ta hanzarta binciken wasu jami’anta dake wuce makadi da rawa wajen cin zarafi da kuma harbi da bindiga ba tare da dalili da wasu jami’an keyi lamarin da wasu lokutan kan jawo asarar rai.

A jihar Taraba kungiyoyin lauyoyi da na kare hakkin dan Adam sun yunkura su tabbatar da an yi adalci biyo bayan harbin da ake zargin wani jami’in hukumar ta DSS a jihar da cewa ya yiwa wani magidanci da bindiga sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu akan hanyar mota.

Cin zarafi, da kisa da kuma wuce gona da iri na wasu jami’an tsaro na cikin matsalolin dake tada hankullan jama’a dama kungiyoyin kare hakkin bani adama a jihar Taraba, batun da masana ke kiran a yi bincike.

Na baya bayan nan shine harbi da bindiga da wani jami’in hukumar tsaro ta DSS, da aka bayyana sunansa da Husseini Dona dake aiki a gidan gwamnatin jihar Taraban, bisazargin cewa ya harbi wani mai sana’ar gyaran AC, Alhaji Audu Aminu Muhammad sakamakon takaddamar da ta hada su a hanyar mota.

Yanzu haka wanda aka harban, Alhaji Audu Aminu Muhammad na kwance a asibiti ana masa jinyar harbin bindigan.

Tuni wannan batu ya kai ga kungiyar lauyoyin jihar Taraban. Barrister Idris Abdullahi Jalo, shugaban kwamitin sa ido kan harkokin kare hakkin dan Adam, na kungiyar lauyoyin jihar ya tabbatar da faruwan lamarin da matakin da zasu dauka.

Shima wani dan rajin kare hakkin dan Adam a jihar Ahmad Gambo Daud, yace abun takaici ne wuce gona da irin da wasu jami’an tsaro ke yi a jihar, inda yace kusan wannan ne karo na biyar da ake samun irin wannan ta’asa na jami’an tsaro.

Yayin da kawo yanzu hukumar DSS a jihar ba tace komi ba, rundunan yan sandan jihar Taraba ta bakin kakakinta David Misal tace ta na bincike.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG