Jam’iyyar APC tayi alkawarin ganin ta bada gudunmowar ta don gudanar da zabe ba tare da wani tashin hankali ba, kome ya dace su yi domin cika wannan alkawarin nasu? Tambayar da muryar Amurka tayi ma Dr. Abbati Bako, masanin harkokin demokradiyya ke nan inda, yace akwai abubuwan da ya kamata a yi a aikace, don gudanar da zabe na gari.
Abu na farko shine a tabbatar da cewa ba a yi amfani da kudi ba ko ‘yan Daba don kauce ma duk wani tashin hankali kafin zabe, ko ranar zabe, ko kuma bayan zabe.
Haka kuma a tabbatar da cewa jami’an da za sa ido wajen zabe na jam’iyyun adawa da mai mulki ba wadanda zasu haddasa fitina ba ne, ko suyi burus da ka’idodin zabe da hukumar zabe ta shimfida.
Dr. Abbati ya kara da cewa bai kamata a yi amfani da jami’an tsaro ba wajen tursasa wa jama’a ranar zabe. In har aka sami fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa da hukumar zabe, kuma a ka bi abubuwan da suka dace, to babu shakka za yi zabe lafiya a gama lafiya inji Dr Abbati.