Ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da aka fitar wacce Sakatare Janar na kungiyar Musulunci ta Jama’atu Nasril Islam, Dr Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu a madadin sarkin.
Sarkin ya yi kira ga Musulmai da su kara mayar da hankali wajen tsaftace kansu domin hana yaduwar cutar.
A cewarsa, “hankalin mu ya tashi sakamakon ganin yadda wannan cutar ke ci gaba da yaduwa a kasashen duniya gaba daya da yadda ta ke yi wa rayukan mutane illa.”
”A yanzu, kowace kasa na daukar matakai kamar killace mutanen da ake kyautata zaton sun kamu da cutar, yayin da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ake kula da su a cibiyoyi na musamman.”
“Kungiyar JNI na kira ga dukannin limamai da su gudanar da addu’o’i na musamman, domin rokon Allah ya yaye mana wannan annobar wato Coronavirus, da kuma sauran cututtuka da ke damun duniya.”
Hakan dai na zuwa kwannaki kadan bayan da aka samu mutum na farko da ke dauke da cutar a birnin Legas da ke Najeriyar.
An kuma killace wasu mutane na daban a kasar, wadanda ake kyautata zaton sun yi mu’amala da wadanda suka shiga kasar daga China da ke zaman tushen bullar cutar.
Har yanzu dai mutum guda ne aka tabbatar yana dauke da cutar a Najeriya.
Facebook Forum