Wani malami ne yana koyar da darasin Hausa, bayan ya kamala bayani sai ya ce bari ya gwada ya ga ko daliban sun fahimci abinda ya koyar. Ashe bai sani ba a cikin wadanda ke zaune a ajin akwai wani mahaukaci.
Da malamin ya ce ina son idan na fadi wani abu daya daga cikin ku ya fada min kishiyar, nan da nan mahaukaci ya daga hannu ya ce zai bada amsa. Malamin ya ce sama sai Mahaukacin yace kasa, Malam yace Ruwa sai Mahaukacin yace Iska, Malam yace Wuta sai Mahaukacin yace Aljanna, Malam yace Malami sai Mahaukacin yace Dalibi, Malam yace mai kudi Mahaukacin yace Talaka, sai malamin yayi murmushi yace amma kana da kokari, sai Mahaukacin yace amma kai dakiki ne.
Malamin ya ga “dalibin” yana neman ya wuce gona da iri sai yace to ya isa haka, sai Mahaukacin yace bai isa ba, Malamin yace kana da hankali kuwa, sai Mahaukacin yace kai ma Mahaukaci ne…
Saurari shirin domin jin cikakken labarin da Hadiza Isa Wada ta aiko mana: