Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Mai Neman Koyan Hausa Na Zamo Babbar Mai Sha'awar Fina-Finai Da Wakokin Hausa


(An sabunta wannan labari da kashi na 2 da na 3 na hira da Carmen McCain)

Watakila idan ka ce Carmen McCain, mutane da yawa ba za su san ko maganar wa ka ke yi ba, amma da zarar ka ce Talatu Danny ko kuma Talatu Baturiya, to nan da nan za ka ji an ce to, Talatu kake nufi? Musamman ga masu shiryawa, ko tsarawa ko fitowa a fina-finan Hausa da mawakan zamani na Hausa, wannan suna ya zamo kamar abin nan da Hausawa ke kira "Gidan kowa da shi."

A yanzu dai, Talatu, daliba a Jami'ar Wisconsin dake garin Madison, tana rubuta takardunta na samun babban digiri na digirgir, ko PhD, a kan fina-finan Hausa da kuma wakoki na zamani da suka zamo ruwan dare a kasar Hausa a wannan lokacin.

Carmen McCain (sunan Talatu na asali ke nan idan ba mantawa aka yi ba) ta fara zuwa Nijeriya tun shekarar 1988, lokacin tana mai shekaru 11 da haihuwa, tare da iyayenta, wadanda har yanzu su na Nijeriya su na koyarwa a Jami'ar Jos. A nan ta fara haduwa da harshen Hausa, ta kuma fara nuna sha'awar wannan harshe.

A cikin hirar da muka yi da ita don filin "A Bari Ya Huce..." malamar ta bayyana yadda ta tafi Sakkwato don koyon harshen Hausa, ta kuma koma Kano domin kara zurfafa wannan nazari nata na adabin Hausa.

Ta ce ta fara kallon fina-finan Hausa a kokarin koyon harshe da kuma al'adun Hausawa, amma nan da nan sai ta kamu da sha'awar wadannan fina-finai da kuma wakokin da ake yi cikinsu har ta zo ga yanke shawarar yin nazari mai zurfi a kan wannan.

A kashin farko na wannan hira da za a iya ji a gefen dama a sama, Talatu ta yi maganar yadda ta fara sha'awar wannan harshe da fina-finai. A yi sauraro lafiya.

XS
SM
MD
LG