Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Falasdinawa Sun Kama Mutane 3 Game Da Harin Bam Na Gaza - 2003-10-17


'Yan sandan Falasdinawa sun kama mutane uku, suna kuma farautar wasu biyu dangane da harin bam da aka kai kan wasu ma'aikatan jakadancin Amurka ranar laraba a zirin Gaza.

Harin ya kashe Amurkawa uku masu gadi, ya kuma sa aka kara matsin lamba kan majalisar mulkin kan Falasdinawa da ta murkushe 'yan kishin Falasdinu.

Wadanda aka kama 'ya'yan wata kungiya ce da ake kira "Popular Resistance Committee" wadda ta ce babu hannunta a wannan harin.

Amurka ta tura wasu kwararrun masu bincike daga Hukumar Binciken manyan Laifuffuka ta tarayya domin taimakawa wajen gudanar da bincike. Shugabannin Falasdinawa sun yi alkawarin bayar da cikakken hadin kai.

XS
SM
MD
LG