Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Afghanistan Da Na Amurkla Sun Gwabza Da Mayakan Taleban - 2003-08-30


Sojojin Afghanistan, tare da goyon bayan sojoji da jiragen kai farmakin bama-bamai na Amurka, sun gwabza na tsawon sa'o'i takwas da wasu mayakan da ake kyautata zaton 'yan Taleban ne a cikin wasu duwatsu dake cikin lungu.

An fara gwabza wannan fada tun ranar alhamis da maraice a yankin Dai Chopan na lardin Zabul dake kudu da Kabul, babban birnin kasar. Jami'an sojan Afghanistan suka ce an kashe mayakan Taleban su fiye da 30.

Rundunar sojan Amurka ta ce an kashe wani sojan kundumbala na Amurka a bayan da ya subuto daga kan dutse lokacin da aka kai wani farmaki cikin dare a kan 'yan Taleban din. Sojojin Afghanistan uku sun ji rauni a wannan fada.

A halin da ake ciki, an kashe sojojin Afghanistan uku jiya Jumma'a a lardin Kandahar, a lokacin da mayakan Taleban suka kai farmaki kan wani wurin da sojoji ke binciken ababen hawa da matafiya a kusa da bakin iyaka da Pakistan.

Rahotanni suka ce an sace wani kwamandan sojojin Afghanistan.

XS
SM
MD
LG