Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Sao Tome - 2003-07-16


Bijirarrun sojoji a tarayyar tsibiran Sao Tome da Principe sun ce sun hambarar da gwamnatin kasar.

A cikin wani sakon da aka yada ta gidan rediyon kasar, wani mutumin da ba a san ko wanene ba ya karanta sanarwar dake cewa shugabannin juyin mulkin sun rushe gwamnati da dukkan cibiyoyinta.

Tun da fari a yau laraba, an ji kararrakin harbe-harbe a Sao Tome, babban birnin kasar, a yayin da sojoji masu juyin mulki suka kame manyan jami'an gwamnati tare da muhimman gine-gine. Ba a samu rahoton mutuwa ko rauni ba.

Sojoji sun kama firayim minista mace ta farko a kasar, Maria das Neves, tare da ministan man fetur, Joaquim Rafael Branco.

An yi imani da cewa manjo Fernando Pereira shine ya jagoranci wannan juyin mulki a daidai lokacin da shugaban kasar, Fradique de Menezes, yake ziyara ta kashin kansa a Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya makwabciyar tsibiran ta yi tur da wannan juyin mulki, ta kuma ja kunnen sojojin Sao Tome da kada su kuskura su taba lafiyar 'yan Nijeriya dake zaune a can. Ita ma Mozambique ta yi tur da wannan juyin mulki.

Wannan tarayya ta Sao Tome da Principe ta kunshi tsibirai da dama a cikin teku kusa da gabar Afirka ta Yamma, kuma tana da mutane dubu 150. tana daya daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya, amma kuma gano man fetur da aka yi cikin tekun kasar ya kara zaman tankiya tsakanin al'ummarta.

XS
SM
MD
LG