Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cutar Shan Inna A Sashen Hausa - 2002-08-05


Hausawa suka ce rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya. Haka kuma, aka ce komai nisan jifa, kasa zata fado.

Duk da jinkirin da muka samu wajen zaben wadanda suka lashe kyaututtukan akwatunan rediyo, agogo da riguna a gasarmu ta cutar shan inna, mun samu nasarar yin hakan a karkashin jagorancin Darenktan Muryar Amurka baki daya, Robert Reilly.

Wadanda suka tallafa masa a lokacin wannan buki, sun hada har da darektar bangaren harsunan Afirka a Muryar Amurka, Gwendolyn Dillard, da darektan shirye-shirye na bangaren Afirka, Negussie Mengesha, da shugaban Sashen Hausa, Sunday Dare, da sauran ma'aikatanmu na Sashen Hausa.

A lokacin wannan buki mai armashi dai, mutane goma suka lashe kyautar riguna. Wadannan mutane sune:

1. Rabia'atu Yan Shibale, matar Dan Maraya Shanawa Shinkafi, akwatin gidan waya 574 Numan Jihar Adamawa, Nijeriya.

2. Yusuf Tijjani, Lamba 1 Whaff Road, jakar gidan waya 2059 Kaduna, Kaduna, Nijeriya.

3.(Babu Suna) Jakar gidan waya 1129 Zariya Jihar Kaduna, Nijeriya.

4. Ibrahim Dan Shugaba Shehu Hodi Kofa, Mataimakin Shugaban 'Yan Kasuwa na Jihar Filato, akwatin gidan waya 144 Bukuru, Jihar Filato, Nijeriya.

5. Ayuba Lawan Taura, NYSC Secretariat, jakar gidan waya 2358 Makurdi Jihar Binuwai, Nijeriya.

6. Alexander B. Angbashim, Registry Dept., College of Arts, Science & Technology, jakar gidan waya 1022 Keffi Jihar Nassarawa, Nijeriya.

7. Mustapha Mai Kayan Miya, akwatin gidan waya 135 Gashua Jihar Yobe, Nijeriya.

8. Abu Sufiyanu Ibrahim Safana, inkiya Ofishin hakimin Safana, yankin karamar hukumar safana Jihar Katsina, Nijeriya.

9. Tahirou Amadou, B.P. 512 Grand Bassam, Cote D'Ivoire.

10. Abdullahi Usman SS 1, Art B, Govt. Day Secondary school, jakar gidan waya 5016 Dutsin Ma Jihar Katsina, Nijeriya.

A bayan wadannan mutanen kuma, wasu guda uku sun samu kyautar agogo kowannensu. Masu agogon, sune:

1. Moude Garba, ECWA Fellowship Church, akwatin gidan waya 02, New Karu Jihar Nassarawa, Nijeriya.

2. Honorable Lawal Ahmed Tudun Iya, inkiya Madawakin Tudun Iya, District Head Office, akwatin gidan waya 1 Funtua Jihar Katsina, Nijeriya.

3. Aliyu Malam Bello, Fundong Rural Council, akwatin gidan waya 6 Fundong, Boyo Division, lardin Arewa Maso yamma, Bamenda, Kamaru.

Wadanda suka zamo zakaru kuwa a wannan gasa ta mu, wadanda kuma zasu samu kyautar akwatunan rediyo, sune:

1. Ishaka Umar Mai Agogo, Bakin Ecobank, BP 54 Malanville, Jamhuriyar Benin.

2. El Paralou Moussa, inkiya Assoumane Yaou, BP 245 Maradi, Jamhuriyar Nijar.

3. M. Shettima Mustapha, akwatin gidan waya 46, Bama Jihar Borno a Nijeriya.

Mun samu dubban wasiku a wannan gasa ta cutar shan inna, kuma daga cikinsu darektan Muryar Amurka, Robert Reilly, ya sanya hannu ya zabo wadanda suka yi nasara.

Muna fata za a ci gaba da sauraronmu, tare da rubuto mana wasiku. Muna kuma yin marhabin da shawarwarin masu sauraronmu a koyaushe.

XS
SM
MD
LG