Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria Da Misra Sun Ce Suna Nan Daram A Bayan Shirin Samar Da Zaman Lafiyar Da Sa'udiyya Ta Gabatar - 2002-03-21


Shugabannin kasashen Sham(Syria) da Misra, sun lashi takobin kokarin ganin dukkan kasashen larabawa sun goyi bayan shirin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, wanda Sa'udiyya ta gabatar, idan an zo taron kolin kasashen larabawa cikin mako mai zuwa a birnin Beirut.

Shugaban Misra, Hosni Mubarak, da takwaransa na Sham, Bashar al-Assad, sun ce wannan shiri na maidowa da Larabawa yankunansu domin a samu zaman lafiya, ya nuna kudurin kasashen larabawa na ganin an cimma zaman lafiya mai dorewa cikin adalci.

Shugaba Mubarak ad shugaba Assad sun bayyana wannan a bayan tattaunawar da suka yi larabar nan a birnin al-Qahira. Har ila yau sun yi kashedin cewa kada a far ma kasar Iraqi a wani bangare na fadada yaki da ta'addanci. Shugaba Bush na Amurka ya bayyana kasashen Iraqi da Koriya ta Arewa da kuma Iran a zaman "ginshikan kawancen muguwar manufa" wadeanda suka dukufa ga kokarin kera makamai na kare-dangi.

A ranar 27 ga watan Maris za a bude taron kolin kwanaki biyu na kasashen Larabawa a birnin Beirut. A farkon makon nan, shugaba Mubarak ya gana da ministan harkokin wajen Sa'udiyya, Yarima Sa'ud al-Faisal, wanda ya ce har yanzu bai ji wata kasar Larabawa ta soki shirin samar da zaman lafiyar na Sa'udiyya ba.

har ila yau, ministan harkokin wajen na Sa'udiyya ya kuma gana da babban sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa mai wakilai 22, Amr Moussa. Mr. Moussa ya shaidawa wata jaridar kasar Italiya mai suna "Corriere della Sera" cewar yana jin za a iya cimma zaman lafiya a cikin watanni shida kawai idan Isra'ila tayi na'am da wannan shirin. Amma kuma Mr. Moussa yayi hasashen cewa Isra'ila zata yi watsi da wannan shiri na Sa'udiyya, sai fa idan Amurka ta matsawa firayim minista Ariel Sharon lamba kan ya amince da shi.

Tsarin wannan shirin ya samu karbuwar Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai.

XS
SM
MD
LG