Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Suka Sace Masuntan Kasar Sin A Gabar Kamaru Sun Nemi Diyya


Mutanen da suka sace masunta bakwai 'yan kasar Sin, ko China, a dab da gabar kasar Kamaru sun bukaci da a biya su kudin fansa akalla dala dubu 15, kimanin Naira miliyan 2 da dubu dari biyu.

Wadannan 'yan satar mutane da suka kira kansu "Africa Marine Commando" sun sace masuntan a cikin yankin ruwan kasa da kasa ranar jumma'a, daidai mashigin ruwan Guinea.

A ranar litinin, jami'an tsaro na Kamaru sun ce 'yan satar mutanen su na neman a biya su kimanin dala dubu 15 zuwa dubu 20 (Naira miliyan 2.2 zuwa miliyan 3). Jami'an jakadancin kasar Sin a birnin Yaounde sun ce za su biya wannan kudi, amma gwamnatin Kamaru ta ce ba ta goyi bayan haka ba.

Kafofin labarai na kasar Sin sun ce sun yi imanin mutanen da aka sace din ba su cikin hatsari. Rahotanni sun ce mutanen da suka sace su su na ba su abinci da ruwa.

Ayyukan fashi cikin teku na karuwa a mashigin ruwan Guinea a Afirka ta Yamma, koda yake bai yi tsanani kamar gabar tekun Somaliya ba. Masu fashin baki sun ce rashin matakan tsaro masu nagarta da kuma karuwar rijiyoyin hakar man fetur sun sa yankin ya zamo wani fage mai alamar romo ga bata-gari.

XS
SM
MD
LG