Sunansa na ainihi shi ne Yakubu Adamu Abdullahi, amma idan ba ka ce DJ Yaks ba, zai yi wuya mutane su gane shi.
Tun lokacin da DJ Yaks ya zamo mai kula da gidan buga wakoki da ake kira "Golden Goose Studios" a Kano, yake fitowa da kade-kade da wakoki iri-iri, kama daga "Najeriya Ta Mu Ce" har ya zuwa wakar nan ta "Ruky" mai sosa zuciya kan yadda samari ke shan kaye wajen neman aure. Koda yake wannan kayen da ake magana cikin wakar ta "Ruky" ta shafi DJ Yaks, ya ce abokinsa ne ba wai shi en ya sha wannan kayen ba. Amma shi din ma dai ya sha kaye.
Shi dai DJ Yaks ya fara koyon waka a hannun Adam A. Zango, sannan ya fada hannun Nazir Ahmad Hausawa "Ziriums".
Kwanakin baya, na samu sukunin wani faifan bidiyo na wakokin DJ Yaks daga faifansa mai suna "Mu Yi Shantu" wanda ya burge ni matuka. Saboda haka na yi tattaki zuwa gidan buga wakoki na "Golden Goose" inda muka zauna muka tattauna da shi DJ Yaks kan wakokinsa.
A sama a gefen dama, za a iya jin kashin farko na hirarmu da shi kamar yadda aka watsa a cikin shirin "A Bari Ya Huce..." na ranar asabar 27 ga watan Fabrairu 2010.