Ana samun karin bayani a game da saurayin na dan Nijeriya wanda ake zargi da kokarin tarwatsa wani jirgin saman kamfanin Northwest ranar jumma'a a birnin Detroit a nan Amurka.
Umar Faruk Abdulmutallab mai shekaru 23 da haihuwa, da ne ga wani sanannen jami'in banki a Nijeriya, Dr. Umar Abdulmutallab, kuma yayi karatu a kasashen Togo da Britaniya.
'Yan'uwansa sun bayyana shi a zaman mai fara'a da basira, yayin da abokansa da suka yi makaranta tare suka ce yana da dangantaka mai kyau da malamai da sauran dalibai.
Amma wadannan mutanen suka ce Umar Faruk Abdulmutallab, wanda mutum ne mai son addini, ya zo ya rungumi wasu ra'ayoyi na tsageranci daga baya. 'Yan'uwansa sun ce abin ya dame su sosai, musamman a cikin 'yan watannin nan, a lokacin da ya tsinke hulda da iyaye da kuma 'yan'uwansa baki daya.
Mahaifinsa ya damu kwarai da yadda lamarin ya kasance har ma ya tuntubi hukumomin tsaro na Nijeriya da ofishin jakadancinA murka Nijeriya inda ya gargade su game da ayyukan dan nasa.
Jami'an gwamnatin Amurka sun ce an sanya sunan Umar Faruk Abdulmutallab a cikin jerin sunayen mutanen da za a sanya musu idanu bisa zaton su na kokarin aikata ta'addanci, amma ba a soke takardar bizarsa ta shiga Amurka ba, haka kuma ba a sanya sunansa cikin jerin mutanen da aka haramtawa shiga jirgin sama a nan Amurka ba.
'Yan'uwansa suka ce sun yi mamaki matuka a lokacin da suka samu labarin cewa yayi kokarin tayar da bam cikin jirgin sama.