Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwallon Kafa Ya Haddasa Rikicin Diflomasiyya Tsakanin Masar Da Aljeriya


Tashe-tashen hankulan da aka yi a tsakanin ‘yan kallo a wasanni biyu na karshe na share fagen zuwa gasar cin kofin kwallon kafar duniya a tsakanin Masar da Aljeriya, sun sa huldar jakadancin kasashen biyu ta yi tsami, yayin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta kaddamar da bincike.

Jiya alhamis, Masar ta janye jakadanta daga kasar Aljeriya bisa zargin cewa magoya bayan Aljeriya sun kai farmaki a kan Misrawa a bayan wasan da aka buga tsakanin masar da Aljeriya ranar laraba a Khartoum a kasar Sudan, wasan da Aljeriya ta lashe da ci daya da babu.

A halin da ake ciki kuma, Hukumar kwallon kafar duniya, FIFA, ta tuhumi hukumomin kwallon kafar Masar dangane da farmakin da aka ce Misrawa sun kai a kan ‘yan wasan kasar Aljeriya kafin wasan da suka yi ranar asabar a al-Qahira, wasan da Masar ta lashe da ci biyu da babu.

Gwamnatin Aljeriya dai ba ta ce uffan ba dangane da wadannan al’amura. ‘Yan wasan Aljeriya da jami’ansu sun ce Misrawa sun yi ta jifar motarsu da duwatsu daga filin jirgin sama zuwa hotel din da suka sauka a al-Qahira, har aka farfasa tagogin motar.

XS
SM
MD
LG