Rundunar sojojin kasar Chadi ta ce ta gwabza sabon fada jiya laraba da ’yan tawaye a gabashin kasar, kusa da bakin iyaka da yankin Darfur na kasar Sudan.
Rundunar sojojin ta ce ta bi sawu, ta kuma kamo ’yan tawayen da suka tsere bayan kazamin fadan da aka yi ranar litinin. Wani kakakin gwamnati ya ce sojoji sun ragargaza sojojin ’yan tawayen, amma kuma babu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskata wannan ikirarin.
Rundunar sojojin Chadi da mayakan ’yan tawaye duk sun yi ikirarin kashe daruruwan abokan gabarsu a kazamin fadan da aka yi ranar litinin a gabas da garin Abeche, gari mafi girma a yankin.
Sabon fada ya barke a bayan wargajewar shirin tsagaita wutar da aka sanya ma hannu a watan da ya shige a kasar Libya, a tsakanin gwamnatin Chadi da manyan kungiyoyin ’yan tawaye hudu.