Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan'uwa Da Abokai Sun Tuna Da Marigayi Ahmad S. Nuhu


Mutane masu dimbin yawa su na ci gaba da yin tururruwa zuwa gidan marigayi Ahmad S. Nuhu a Kano, domin yi wa iyalansa da 'yan'uwansa ta'ziyya.

Rahotannin da ke isowa filin "A Bari ya Huce..." sun ce kusan dukkan masu harkar fina-finan Hausa, mazansu da matansu, sun yi zaman karbar gaisuwa a gidan marigayin, inda daruruwan mutane daga sassan Nijeriya dabam-dabam suka yi ta zuwa gaisuwa. Wasu daga cikinsu ma sun ce ba su taba ganin jarumin ido da ido ba, amma mutuwarsa ta girgiza su.

A cikin wannan kashin farko na shiri na musamman domin tunawa da matigayi Ahmad S. Nuhu, filin "A Bari Ya Huce..." ya tattauna da matar marigayin, Hajiya Hafsat A.S. Nuhu, wadda ta yi bayanin abubuwa na al'ajabi da take gani tun bayan rasuwar mijin nata.

Sauran wadanda za a iya ji cikin kashin farko na shirin sun hada har da Baballe Hayatu, Farida Jalal, Fati Mohammed, Abba al-Mustapha, Alhaji Yakubu Lere, Ishaq Sidi Ishaq, Rashida Adamu Abdullahi, da kuma Abubakar Araba.

Sai a matsa rubutun dake saman wannan labari domin a ji cikakken shirin farko na ta'aziyyar, ko kuma a yi kofensa cikin na'ura.

XS
SM
MD
LG