Jami'an gwamnatin Nijeriya sun ce tsohon shugaban kasar Liberiya, wanda ake tuhuma da aikata laifuffukan yaki, Charles Taylor, ya bace daga gidan da byake zaman gudun hijira ciki a Nijeriya.
Suka ce a cikin daren litinin ne Taylor ya sulale daga gidan da gwamnatin Nijeriya ta ba shi a birnin Calabar.
Mr. Taylor ya sulale ya bace jim kadan a bayan da gwamnatin Nijeriya ta ce a shirye take ta kyale gwamnatin kasar Liberiya ta kama shi.
Kotun bin kadin laifuffukan yaki ta Majalisar Dinkin Duniya a Saliyo ta nemi da a kama Mr. Taylor bisa tuhumar fyade da gana azaba a lokacin mulkinsa da kuma lokacin yakin basasar da aka yi a Saliyo makwabciyar Liberiya.