Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta-Kifen Niger Delta Sun Ce Ba Zasu Tattauna Da Jami'an Shiga Tsakani Na Gwamnatin Nijeriya Ba


'Yan ta-kifen dake yin garkuwa da ma'aikatan mai hudu a Nijeriya sun ce ba zasu tattauna da masu shiga tsakani na gwamnatin Nijeriya ba, sun kuma nanata barazanar kaddamar da sabbin hare-hare.

'Yan fashin mutanen sun ce ba su amince da masu shiga tsakani na gwamnatin ba, kuma ba zasu tattauna ko yin hulda da su ba.

Wadannan kalamu nasu sun yi sabani da na jami'an gwamnatin Nijeriya wadanda suka ce gwamnati tana tuntubar 'yan fashin mutanen kuma tana da kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba za a sako 'yan kasashen wajen da ake yin garkuwa da su.

Jiya asabar, ministan yada labarai na Nijeriya, Frank Nweke, ya musanta rahotannin da 'yan ta-kifen suka bayar cewa daya daga cikin mutanen da suke yin garkuwa da su ba ya da lafiya sosai. Suka ce za su kashe sauran mutane ukun da suke garkuwa da su idan maras lafiyar ya mutu.

'Yan fashin mutanen sun bukaci da a sako wani madugun 'yan daba na yankin dake kurkuku tare da wani gwamnan da aka tumbuke. Har ila yau su na neman a biya su diyyar gurbata yankin tare da mika ikon tafiyar da albarkatun wannan yanki ga mutanensa.

XS
SM
MD
LG