Korea ta Arewa tace ba zata daina shirinta na kirar makaman nukiliya ba sai lokacin da ta sami kundunan samar da makamashin wutar lantarki ko kuma a bata su. A yau Talata kafofin labarun Korea ta Arewa suka yayata wannan sanarwa. Ba’a tantance dada ko Korea ta Arewar, tana neman kaucewa alkwarin da ta dauka ne a babban taron birnin Beijing na jiya litinin ba. Shugaba Bush na Amurka, ya yaba da alkawarin da Korea ta Arewar tayi jiya litinin a taron kolin, amma yace wajibi ne aje a duba domin tabbatarwa. Korea ta Arewa tace a shirye take ta baiwa jami‘an kasa da kasa damar zuwa su ganarwa idonsu, amma sai an saka mata da agajin tattalin arziki tukuna.