Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Britaniya Sun Ce Sun Kama Karin MUtane Bakwai Yau Lahadi


'Yan sandan Britaniya sun ce sun kama karin mutane bakwai a yau lahadi dangane da yunkurin da aka yi na kai hare-hare kan ababen sufuri an London a ranar 21 ga watan yuli.

An kama mutanen ne a lokacin da aka binciki wasu gidaje biyu a yankin Sussex na kudancin Ingila.'Yan sanda ba su bayar da karin haske a game da irin hannun da ake zargin mutanen suna da shi a hare-haren bam din da suka ci tura ba.

Tuni an kama mutane hudun da suka yi niyyar kai wadancan hare-haren bam, guda uku a London na cikon hudun kuma a kasar Italiya. A yanzu masu bincike sun mayar da hankali a kan amsu taimakawa mutanen.

A halin da ake ciki, 'yan sandan Italiya sun ce sun kama wani dan'uwan mutumi na hudu da ake zargi da kulla kai hare-haren bam din na London, Osman Hussain, bisa zargin takardun jebu. A ranar jumma'a a birnin Rum 'yan sanda suka kama Hussain kuma ana sa ran zai ki yarda da kokarin da Britaniya take yi na a mika mata shi.

Har ila yau a ranar jumma;a an kama wani dan'uwan shi Hussaini a Rum bisa zargin bayar da mafaka ga mutumin da ake zargi da kulla harin bam da kuma mallakar takardun jebu.

XS
SM
MD
LG