Shugaba Bush Da Shugaba Tandja tare da sauran shugabannin Afirka a fadar White House |
Mr. Bush yayi magana yau litinin a nan Washington a bayan da ya gana da shugaba Tandja Mamadou na Jamhuriyar Nijar tare da shugabannin kasashen Botswana, Ghana, Mozambique da kuma Namibiya.
Shugaba Bush ya yabawa shugabannin biyar a zaman 'yan rajin dimokuradiyya da suka rungumi damar cin moriyar dokar da Amurka ta kafa ta Karfafa Cinikayya da Samar ad Dama ga kasashen Afirka.
Wannan dokar da aka kafa a 2000, ta bai wa kasashen Afirka karin damar sayar da kayayyakinsu a aksuwannin Amurka idan har za su ringa yin mulki bisa doka tare da kare hakkin bil Adama.
Mr. Bush ya ce shugaba Tandja Mamadou da sauran shugabannin hudu suna yin haka, yana mai lura da cewa a shekarar da ta shige, yawan kayayyakin da kasashen Afirka ke kawowa nan Amurka ya karu da kashi 88 daga cikin 100.
Har ila yau Mr. Bush ya sake jaddada alkawarin kara yawan agajin da Amurka take bai wa Afirka tare ad soke bashin dala miliyan dubu 40 na kasashe 18 da suka fi talauci a duniya, akasarinsu daga nahiyar Afirka.