Da yake bayani ga manema labarai ta wayar tarho, Peskov ya yi nuni da kalamai daga Putin a ranar Alhamis, wanda yake cewa Amurka tana da cancantar taimakawa shirin tsagaita wutar tsakanin Rasha da Ukraine tsawon kwanaki 30 amma ya ce akwai wasu tambayoyi dake bukatar amsoshi.
Peskov ya ce yayin da ya rage abubuwa da dama da ya kamata a yi, Putin ya bayyana gamsuwarsa ga matakin da shugaban Amurka Donald Trump ke dauka. Ya ce Putin ya yi wata ganawar cikin dare da wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff a ranar Alhamis, lokacin da Putin ya mika sakwannin bayanai da alamomi ga shugaba Trump.
Kakakin na Kremlin ya ce dukkan bagarorin sun amince Putin da Trump su tattauna, inda ya kara da cewa za a saka lokacin tattaunawar da zarar Witkoff ya isar da manzancin sabbin bayanan ga Trump.
Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social da safiyar ranar Jum’a cewa, a karshe akwai babbar dama ta kawo karshen wannan mummunan yaki na zub da jinni zuwa karshe.
Da yammacin ranar Juma’a ne Putin ya shaidawa kwamitin tsaron kasar a birnin Moscow cewa idan sojojin Ukraine suka ajiye makamansu suka mika wuya, to ba za a kashe su ba.
Sai dai rundunar sojin Ukraine ta musanta cewa sojojin Moscow sun killace dakarunta da ke Kursk, kuma sun ce rahotannin da ke tabbatar da hakan na Rasha ne.
Dandalin Mu Tattauna