Harin ya auku a garin Falasdinawa na Al-Funduq, daya daga cikin manyan titunan dake tsallaken yankin gabas maso yammacin yankin.
Laftanar Janar Herzi Halevi yace, "Ga ‘yan ta’addan da suka kai harin, dubunsu ya kusa cika. Za mu gano ko su waye su ka yi wannan aika-aikar kuma zamu cimmu su. Za mu yi maza mu wuce wannan garin dake kan wannan hanyar sannan za mu inganta tsaro akan hanyar.”
Kungiyar agajin Isra’ila ta Magen David Adom ta ce, mata biyu da suka zarta shekaru 60 da wani mutumin da ya shekarun shi suka zarta 40 aka kashe a hadarin.
Tashin hankali ya karu a yankin tun bayan harin bazata da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ya rura rikicin da ake ci gaba da gwabzawa a Gaza.
Dandalin Mu Tattauna