Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ghana Nana Akufo Ado Ya Sha Suka Bayan Kaddamar Da Mutum Mutumin Sa


Ghanian President Nana Akufo-Ado Statue
Ghanian President Nana Akufo-Ado Statue

Shugaban kasar Ghana mai barin gado Nana Akufo-Addo, yana fuskantar kakkausar suka a shafukan sada zumunta bayan da ya kaddamar da wani mutum-mutumi sa a harabar wani asibiti a yankin yammacin kasar.

Yusuf Fufuano, babban jami'i a ma'aikatar sadarwa na kasar ta Ghana, ya bayyana ma wakilin Muryar Amurka a Kumasi Hamza Adams cewa manufar kaddamar da mutumum mutumin ita ce don al'umma ta samu abin tunawa da irin ayyukan raya kasar da shuagban yayi a wa'adin mulkin sa 2 na shekara 8. Ya kuma kara da cewa, alummar yankin sun samar da mutum mutumin ne bayan la'akari da yadda shugaba Akufo-Ado ya jajirce ya taimaka ya kawo gudanar da ayyukan raya kasa a yankin da duk gwamnatin baya suka kasa basu kulawa.

Wasu al'umar kasar sun yiwa wannan matakin da shugaban ya dauka fassarar tallata kansa maimakon yiwa jamma’ar kasa hidima, musamman ma la'akari da yadda ake fama da tsadar rayuwa a kasar.

Wani dan majalisa a babbar jam'iyyar Adawa Emmanuel Ama Kofi Bua, wanda ya wallafa a shafinsa na X cewa, al'ummar kudancin Ghana sun cancanci fiye da wannan mutum mutumi sannan wannan aikin son kai ne kawai.

A saurari sautin rahoton Hamza Adams:

RAHOTON CECE KUCE AKAN GINA MUTUM MUTUMIN SHUGABAN GHANA .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG