Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewar sabanin abinda jama’a ke hasashe, yana karbar naira miliyan 25 ne a matsayin kudaden alawus dinsa lokacin da yake rike da mukamin.
Dogara wanda ya wakilci mazabar tarayya ta Bogor/Dass/Tafawa Balewa daga jihar Bauchi, ya rike mukamin Kakakin Majalisar Wakilai tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019.
Sai dai, bai fayyace ko alawus din naira milyan 25 din na wata ne ko shekara ko kuma na ilahirin shekaru 4 daya shafe a majalisar wakilan ne ba.
A jawabinsa yayin wani taro a Abuja a yau Laraba, Dogara ya bayyana mamakin daga inda maganar cewa ‘yan majalisar tarayya na daukar makudan kudade a matsayin albashi ta fito.
Ya ce “gaba dayan kudin alawus dina a matsayina na Kakakin Majalisa Naira miliyan 25 ne, a wancan lokaci. Na umarci akantana ya bude wa kudaden asusun ajiya saboda ba nawa bane.”
“Ko yanzu da muke batu akan kudaden alawus din, al’umma na kallonsu a matsayin makude, ina neman gafararka kakakin majalisa, ina kuma neman gafarar majalisar ita ma.”
Dandalin Mu Tattauna