SOKOTO, NIGERIA - Da ma Sarukan sun jima suna dakon sakamakon bincikensu da gwamnatin ke yi, sai dai wasu jama'a musamman na bangaren adawa na ganin bita da kulli ne gwamnatin ta yi musu.
Kakakin gwamnatin jihar Sakkwato Abubakar Bawa ya ce wadanda aka sauke daga mukamansu sun hada da uwayen kasar Unguwar Lalle, Yabo, Wamakko,Tulluwa, Illela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu da na Giyawa.
Haka kuma an tube wasu uwayen kasa shida akan dalilin cewa lokacin da aka nada su an yi gaggawa ba a bi ka'ida ba. Sai kuma wasu biyu da aka sauya wa wurin aiki wadanda daya daga cikinsu ‘dan majalisar sarkin Musulmi ne, da sabon magajin gari da aka mayar a kan sarautar sa ta da, yayin da za a ci gaba da gudanar da bincike akan wasu uwayen kasar hudu.
Har ila yau an amince da wasu uwayen kasa tara dadaga cikin wadanda aka bincika akan su ci gaba da aikinsu.
To sai dai wasu jama'ar jiha musamman na bangaren jam'iyar adawa ta PDP na ganin wannan bai zo da mamaki ba domin da ma a cewar su wannan gwamnatin ta kuduri cin zarafin sarakuna iyayen al'umma.
Hassan Sahabi Sanyinnawal kakakin janm'iyar ta adawa ya ce rashin sanin aiki ne gwamnati ta ce an nada wasu sarakuna ba bisa ka'ida ba.
Amma kuwa kakakin gwamnatin jihar Sakkwato kuma kakakin jam'iyar APC mai mulki Sambo Bello Danchadi ya ce abinda gwamnati ta yi kan ka'ida yake.
Yanzu dai jama'a na ci gaba da tofa albarkacin bakin su akan wannan lamarin, wasu na ganin an yi daidai, duba da dalilan da aka bayar na tube sarakunan wasu kuma na ganin akasin haka, yayin da sauran uwayen kasa hudu da ake ci gaba da bincike ke dakon jin na su sakamako.
An jima dai ana zargin sarakuna da tsoma hannu ga lamurran siyasa a Najeriya abinda kuma wasu lokuta yakan zo musu da mummunan sakamako.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna