Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: *Maik Taison (Mike Tyson) Bai Mutu Ba - Dakta Babikwai


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Dr Adamu Babikwai, malami a kwalejin horas da malamai ta gwamnatin tarrayya da ke Yola, (ko FCE Yola), Adamawa Najeriya, ya tabbatar cewa tsohon shahararren dan damben zamanin nan, Mike Tyson, bai mutu ba, sabanin wani labarin wanda wasu anan Amurka su ka kirkiro, su ka kuma yada shi kwanan baya, tamkar gaskiya, wanda har ya samu shiga cikin amsoshin da su ka gabata kan Mike Tyson, wanda shi Dr ya bayar.

To, don masu sauraro su samu cikakke, kuma sahihin bayanin Dr Babikwai kan tarihin Mike Tyson, za mu gabatar ma ku da ingantacciyar amsar Dr Babikwai, ga tambayar ta Alh Umar Forever, kan tarihin Mik Tyson, kamar yadda wakilinmu a Adamawa/Taraba, Muhd Salisu Lado, ya turo.

A sha bayani lafiya:

12-09-23- AMSOSHIN TAMBAYOYINKU - Mike Tyson Bai Mutu Ba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG