Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shiri na Amsoshin Tambayoyinku.
Tabaya 1:
"Salam Sashin Hausa Na VOA. Don Allah Ku tambaya ma na malaman addinin Islama. Wai Shin ta ina lefe ya samo asali? Kuma za mu so jin wai shin wajibi ne ga kowane dan adam a auren addinin Islama?"
Mai Tambaya: Sani Gulle Kampala, Malam-madori jahar Jigawa, Najeriya
Tambaya 2:
Za kuma a ji ci gaban tambayar nan mai cewa: “Salama a laikum VOA Hausa. Shekarun baya kun taba bada tarihi mai ban sha’awa na Kofofin Kano. Ni ma ina so a ba ni cikakken tarihin kofofin Birnin na Kano. Mene ne dalilin yinsu? Yaushe aka yi su?”
MAI TAMBAYA, idan an tuna, shi ne : Sama’ila Abubakar, Kano.
AMSASOSHI
To bari mu fara da amsar tambaya kan laifen aure a Musulunci. Idan mai tambayar, Malam Sani Gulle Kamfala, da ma sauran ma su sha’awar ji, na tare da mu, an dace mun samu Shugaban Majalisar Malaman Izala Shiyyar Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, kuma Wakilin Malaman Bauchi, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, wanda ya yi cikakken bayani.
Sai kuma kashi na biyu na amsar tambayar Malam Sama’ila. Idan an tuna wakilinmu a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari, ya samo amsar ne daga Farfesa Tijjani Muhammad Naniya na Sashin Tarihi na Jami’ar Bayero ta Kano, wanda ya ci gaba da bayani.
A sha bayani lafiya:
Dandalin Mu Tattauna