Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Mene Ne Tarihin Zababben Shugaban Najeriya Bola Tinubu? Mene Ne Amfanin Tashar Kan Tudu?


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Yau ma mu na tafe da amsoshin tambayoyi masu kayatarwa - Kama daga tambayar da ta shafi tarihin zababben Shugaban Najeriya zuwa wadda ta shafi tashar jirgin ruwa ta kan tudu.

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku.

TAMBAYA: "Don Allah VOA Hausa, muna son a ba mu sahihin tarihin sabon Shugaban Najeriya, Bola Tinubu."

Masu Tambaya: Bashar Maigyaran Rediyo Kamba, da Salihu Isah Fana da Garba Nahali Kamba. Sauran wadandan su ka yi tambaya makamanciyar wannan sun hada da Alhaji Umar Forever da Adamu Adam Gashua.

TAMBAYA ii “Muryar Amurka so nake ku yi min karin haske akan Dala Inland Dry Port, wanda Shugaba Buhari ya bude a jihar kano. Wai shin ta yaya wannan tasha za ta ke gudanar da ayyukanta? Wani alfanu yankinmu na arewacin Najeriya zai samu daga wannan tashar??”

Mai Tambaya: Ado Turaki Askira, Jihar Bornon Najeriya.

AMSA: To, dayake an ce lokacin abu a yi shi; bari mu fara da amsar tambaya kan tarihin zababben Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Idan masu tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, za a ji abin da ya saukaka daga wakilinmu a Legas, Babangida Jibri.

AMSA ii: Sai kuma amsar tambaya kan alfanun busasshiyar tashar jirgin ruwa, ko tashar kan tudu ta kayan jirgin ruwa, wadda Shugaban Najeriya Buhari ya bude kwanan baya a kano, mai suna Dala Inland Dry Port a Turance. Idan mai tambayar da ma sauran masu sha’awar ji na tare da mu, za a ji amsar da wakilinmu a Adamawa, Muhd Salisu Lado, ya samo daga Dr Adamu Babikwai na Kwalejin Horas da Malamai mallakar Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke Yola, Adamawa, Najeriya, wato FCE Yola.

A yi saurare lafiya:

03-04-23 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU - ok.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:09 0:00

XS
SM
MD
LG