Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya: Takaddama Kan Gonar Zinari a Jihar Yobe


Sarfilu Hashiim Gumel
Sarfilu Hashiim Gumel

A wannan makon mun waiwayi batun gonar zinari a Damaturu jihar Yobe da shirin Ciki Da Gaskiya kawo a baya, inda shugaban kwamitin sulhu na jihar Sheikh Babagana Kyari ya zauna da bangarorin biyu da ke takaddama kan mallakar sashen gonar da a ke batun akwai zinari a ciki.

An tashi daga zama, wanda ya ce ya sayi gona Zakari Usman ya ce shi dai sai dai a gamu a kotu, su kuma masu mallakar gona na ainihi su ka ce ba su da karfin zuwa kotu, amma ba za su taba amincewa da sarayar da hakkin su ba.

Musa Umar a madadin wadanda su ke mallakar gona na ainihi ya ce bukatar sui ta ce a bar mu su sashen da mahaifin su ke da ajiyar wannan dukiya.

Saurari shirin cikin sauti:

Ciki Da Gaskiya: Takaddama Kan Gonar Zinari a Jihar Yobe - 11'38"
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:38 0:00

XS
SM
MD
LG