Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Wasa Paul Pogba Zai Fara Taka Leda A Klob Din Manchester


Dan wasan kwallon kafa na tsakiya a Kungiyar Manchester United dake kasar Ingila Paul Pogba ya ce babu wani bambanci tsakanin Manchester United da tsohowar kulob din Juventus a wurinsa.

A yau Laraba ne Juventus za ta karbi bakuncin Manchester United cikin gasar zakarun Turai a matakin wasan rukunin zagaye na daga rukunin (H).

Indai ba'a manta ba a watan jiya ne kulob din Juventus ta doke Manchester United a gidanta da ci 1-0 a karawarsu na farko da suka buga a gasar ta zakarun turai.

Dan wasan Pogba ya koma Manchester United ne daga Juventus a
shekara ta 2016 a kan zunzurutun kudi har fam miliyan 89, a matsayin
dan kwallon mafi tsada a shekarar.

Pgoba ya bayyana cewa rukunin H rukunine mai tsauri da kuma sosa rai
musammam ma a bangaren shi.

Wasan da zanyi yau a gidan Juventus wani abu na dade ina son gani, Domin a can ne na fara wasa kuma ina girmama kungiyar ta Juventus matuka.

Domin filin wasan gidana ne domin idan ina wasa a filin zanji tamkar ina gida, Pogba zasu hadu da tsohon danwasan Manchester United Cristiano Ronaldo wanda shi kuma ya koma Kungiyar Juventus daga Real Madrid.

Wasan na yau dai za'a fafatane da misalin karfe tara na yammaci agogon Najeriya, Nijar, kamaru da kasar Ghana.

Shi kuwa danwasan gaba na Manchester United Romelu Lukaku ba zai samu damar buga wasan ba saboda rauni da yake fama da shi, domin bai fafata a wasan da Manchester United tayi da Bournemouth ba sabi da wannan raunin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG