Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Afghanistan Sun Kai Ziyara Pakistan


Jami'an Tsaron Afghanistan
Jami'an Tsaron Afghanistan

Wasu kusoshin tsaro daga Afghanistan sun kai ziyarar ba-zata kasar Pakistan domin su tattauna da takwarorin su soja da farar hula kan muhimmancin hada kai ga batutuwa da suka shafi kasashen biyu, biyo bayan munanan hare-haren da Taliban da wasu mayakan sakai suka kai cikin 'yan kwanakin nan a Afghanistan.

Ziyarar ta yau laraba ta zo ne sa'o'i bayan kiran da mukaddashin sakataren harkokin wajen Amurka John Sullivan yayi wa shugabannin kasar ta Afghanistan cewa akwai bukatar su na tuntubar juna da tattaunawa da takwarorinsu na Pakistan.

Samun karin tashe-tashen hankula da tarzoma a Afghanistan shine ya kara ruruta zaman dar-dar tsakanin hukumomin Afghanistan da Islamabad, har zargin cewa mayakan sa kai su na amfani da maboyarsu a Pakistan wajen kitsa hare haren da aka akai a Afghanistan a baya bayan nan, tare da taimakon hukumar leken asirin Pakistan.

Hukumomin kasar Pakistan sunyi Allah waddarai da harin ‘yan ta'adda, tare da yin fatali da sukar da Afghanistan keyi mata a matsayin abu mara makama balle tushe, tana cewa akwai bukatar a gudanar da kwakkwaran bincike game da wadannan hare hare.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG